15 Faburairu 2025 - 17:48
Lebanon: Akwai Lauje Cikin Naɗi A Sabuwar Gwamnati

Wannan rahoton yana dauke da bidiyoyin yadda jami'an tsaron kasar Labanon suka fesa barkonon tsohuwa akan taron lumana na masu zanga-zangar kin amincewa da hana sauka da tashin jiragen kasar Iran.

Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta kira taron jama'a da yammacin yau a tsohon titin filin jirgin sama na Beirut domin nuna adawa da tsoma bakin gwamnatin sahyoniyawa a cikin harkokin kasar Labanon da kuma take hakkin kasar.

Yayin da jama'a ke kara yawa a wajen tarin, sojojin kasar Labanon sun kai hari kan taron lumana tare da harba hayaki mai sa hawaye a lokacin da Abbas Qamati mataimakin shugaban majalisar siyasar Hizbullah ya ke jawabi.

A karshe dai kungiyar Hizbullah ta sanar da kawo karshen taron tare da cewa: "Saƙonmu Ya Isa. Muna son a yi jana'izar Sayyid Hasan bisa wayewa ne".

Firaministan na Lebanon ya kuma ce: Tsaron filin jirgin ya fi komai, ba za mu bari a yi sakaci a wannan fanni ba, kuma dole ne jami'an tsaro su shawo kan tashe tashen hankula.