Wani bangare na fassara daga cikin hudubar sallar Juma'a na wannan mako a birnin Aalishahr da ke lardin Bushehr, a ranar 10 ga watan Junairu, 2025, da Hujjatul Islam Hamidinejad, limamin Juma'a na wannan birni ya gabatar:
Bisa la'akari da cewa muna jajibirin maulidin Imam Ali (AS) mai albarka, kuma na ranar uba, zan so in yi bayani kadan game da kebantaccen yanayi na Amirul Muminin Ali (AS) wanda bayi da tamka: daga cikin abubuwan da Imam Ali as ya keɓanta da su wanda Allah Ta'ala bai bawa wanin sa ba hatta annabawansa Babu wanda ya bawa ita, shine haihuwarsa da akayi a dakin Ka'aba, wanda dukkan malaman Shi'a da Sunna suka yarda da hakan, kuma hakan yana nuna girman matsayinsa a wajen Allah. A lokacin da Sa'asa'ata ɗan Sawhan ya tambayi Ali (a.s) cewa, "Shin kai ne kafi fili ko Annabi Isa As?" Sai ya ce mahaifiyar Isa As yayin da ta kasance tana bautar Allah a Urushalima sai alamun haihuwa suka zo ma ta, sai taji wata murya ta kirata da cewa, "Ki fita daga nan wajen nan gidan ibada ne, ba wurin haihuwa ba". Amma Ni Mahaifiyata Fatima yar Asad yayin da ta ke wajen ka'aba ta roki Allah ya saukaka mata yanayin haihuwarta sai taji mai kira yana cewa ki shigo cikin dakin sai bango ya tsage sai aka haife ni a tsakiyar Ka'aba, kuma mahaifiyata ta kasance baƙuwa ga Allah har na tsawon kwana uku, kuma wannan falala ba ta dace ga wani da ya gaba ce ni ba da wanda zai zo a bayana ba.
Tambaya ta taso kan dalilin da ya sa Allah ya sanya Ka'aba ta zama wurin haihuwa ga Ali (a.s.) - sai mu ce - daya daga cikin mashahuran marubutan Ahlus Sunna, Abdul Fattah Abdul Maqsood, yana cewa tunda dukkan musulmi suna yin salla ne suna masu fuskantar Ka'aba, ta haka ne Allah ya so musulmi su rika tunawa da Ali (a.s.). To ni kuma ina mai cewa menene muhimmancin da ke tattare da tunawa da Ali (a.s.) da tabbas ambaton Ali (a.s) yana da muhimmiyar alaka ga samun rabon dacewa ko kuma samun taɓewa ga musulmi da har zai sa Allah Ta'ala ya zartar da hakan. Idan muka yi la'akari da ayoyin Alqur'ani da kuma ruwayoyi za mu gane cewa lallai Imam Ali (a.s) yana da alaka kai tsaye da musulmi na samun dacewarsu ko taɓewarsu cewa idan har ba su karbi shugabancinsa ba, to za su kasance cikin taɓaɓɓu, idan kuma suka karɓi hakan to zasu kasance cikin masu rabauta.
Haka nan kuma Allah Ta'ala ya gabatar da shi a matsayin kayin ma'aiki - انفسنا- a cikin ayar Mubahala, yana nufin idan wani bai karbi waliccinsa ba, to shi bai karbi manzancin Annabi ba, kuma su biyun ba su rabuwa. Idan har wasu suka ce “ Mu Mun yarda da Annabi, ba mu yarda da Ali (AS) ba, kuma a lokaci guda su ce mu Musulmai ne, Allah shi ma ya karbe mu a matsayin Musulmi, a’a ba haka abun ya ke wannan musuluncin bai cika ba, Musulunci cikakke shi ne abin da Manzo ya fada a ranar da ya gabatar da Ali (AS) shi ne cikakken addini, ya zama addinin ya hada da Amirul Muminin Ali (AS) a kusa da Manzon Allah {Sawa}.

