Kisan Beit Lahia na daga cikin ci gaba da yakin kisan kiyashi da gwamnatin mamaya ke yi wa al'ummarmu sakamakon rashin amincewa na rashin kunyar Amurka da rashin zartar qudirin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya dauka na dakatar da wannan ta'asa.
Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As ABNA ya habarta cewa: A ci gaba da aikin kawar da tsatso da kisan kiyashin da Amurka da Isra'ila ke ci gaba da yi a arewacin zirin Gaza, da sanyin safiyar yau ne wannan makiya ta 'yan ta'adda ta yi ruwan bama-bamai a wata unguwa da ke kusa da asibitin Kamal Udwan da ke birnin Beit Lahia, kuma bisa kididdigar da aka yi, sama da mutane 90 ne suka yi shahada kuma mutane da dama sun jikkata tare da bacewar wasu da ba a san adadisu ba.
