Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As ABNA ya habarta bisa nakaltowa daga tashar sadarwa ta Aljazeera a safiyar yau alhamis cewa bayan fitar da sanarwar ficewa daga yankin Hare Harik da ke kudancin Dahiya, gwamnatin yahudawan sahyuniya ta kai musu hari da munanan hare-hare ta sama.
A cewar majiyoyin na Lebanon, sau 3 jirgin yaƙin gwamnatin sahyoniyawan suka kai hari a kudancin birnin Beirut a safiyar yau ɗin.
