Imam Sadik (a.s) ya ce mahaifinsa ya ce game da tsarin tarbiyya:
“Babana Imam Muhammad Bakir (a.s.) ya kasance yana tara mu yana bukatarmu mu da
mu rika zikirin Allah har zuwa fitowar rana, wadanda ackinmu suke da ikon
karanta Alkur'ani sai ya umarce su da su karanta shi, wadanda kuma ba su da
damar iya karanta Alkur’ani sai ya ce da su su yi ta zikirin Allah.
Ya zo a cikin ayoyi da ruwayoyi cewa abun sone kuma yana da matukar muhimmanci karanta addu’o’i da zikiri bayan sallolin farilla, wadanda wadannan addu’oi ana la’akari da su a matsayin “Ta’aqibar sallah”, wato addu’oi da suke zuwa bayan yin sallah kaitsaye haka nan kuma Allah yana son cewa yayin da idan bawansa ya bi umurninsa ya yi sallah ya roki Allah wani abu da to ya bas hi wannan abun da ya roka. Ana so bayan sallar asuba har rana ta fito, mutum ya shagaltu da yin addu'a da karatun Alqur'ani.
Madogara Al-Wasa’ilish Shia, juzu'i na 4, shafi na 1185, ruwaya ta 1.