9 Nuwamba 2024 - 16:39
Bidiyon Yadda Isra'ila Ta Kai Hari Makarantar Da 'Yan Gudun Hijirar Gaza Suke

Wannan bidiyon yana dauke da irin ta'addancin da barnar da harin da Isra'ila ta kai a wata makaranta kuma matsugunin 'yan gudun hijira a unguwar al-Tuffah da ke Gaza.

Bidiyon ya nuna mummunan halin da muguwar gwamnatin sahyoniyawan ta haifar a harin da ta kai a makarantar Fahad al-Sabah da ke unguwar Al-Tuffah da ke gabashin birnin Gaza, wanda ya kai ga shahada da jikkata wasu 'yan gudun hijirar Palasdinawa da ba su ji ba ba su gani ba.