2 Nuwamba 2024 - 19:34
Salon Rayuwar Ahlul Baiti|Karya Itace Ƙofar Zunubai!  Sakamakon Giba A Lahira

Lokacin da ya fita sai ya sami wasiwasi a zuciyarsa nay a aikata aikin da ya sabwa mutuncinsa, amma nan take ya yi tunanin cewa idan Annabi (SAW) ya tambaye shi wannan gobe idan ya ce bai yi irin wannan aikin ba, to yayi karya. kuma idan ya fadi gaskiya, za a yi masa haddi, hakan kuma za ayi masa akan sauran ayyukan da ba daidai ba, wannan yin tunanin da barin karya yayi shine ya zama tushen barin dukkan zunubansa.

Wani mutum ya zo wajen Annabi (SAW) ya ce: “Ba na yin Sallah, kuma ina aikata wani aiki na zubar da mutunci, kuma ina yin karya! Wanne zan fara bari?!

Annabi (SAW) ya ce: Karya zaka bari, kuma ya yi alkawari a gaban Annabi (SAW) ba zai taba yin karya.

Lokacin da ya fita sai ya sami wasiwasi a zuciyarsa nay a aikata aikin da ya sabwa mutuncinsa, amma nan take ya yi tunanin cewa idan Annabi (SAW) ya tambaye shi wannan gobe idan ya ce bai yi irin wannan aikin ba, to yayi karya. kuma idan ya fadi gaskiya, za a yi masa haddi, hakan kuma za ayi masa akan sauran ayyukan da ba daidai ba, wannan yin tunanin da barin karya yayi shine ya zama tushen barin dukkan zunubansa.

Tafsir Namuneh, juzu'i na 11, shafi na 413.

Sakamakon Giba A Lahira

Manzon Allah (SAW) yana cewa:

A ranar kiyama za a gabatar da mutum a gaban Allah a ba shi littafin ayyukansa, amma ba zai ga ayyukansa na alheri a cikinsa ba.

Sai ya ce: Ya Allah! Wannan ba littafina ba ne, domin ban ga biyayya da ibadar nayi a cikinsa ba!

Sai Allah Ta’ala ya ce da shi: Ubangijinka ba ya kuskure kuma ba ya mantuwa, ayyukanka sun lalace ne saboda gibar da kaiwa mutane, sai su zo da wani mutum su ba shi littafin ayyukansa, a cikinsa akwai yawaita ayyukan da’a da ibada.

Ya ce: Allah! Wannan littafin ba na aikina bane, domin ban yi yawan ibada ba! Sai Allah ya ce masa: Hakane wane ne yayi gibarka saboda haka muka baka kyawawan ayyukansa.

Mustardakil-Wasail, juzu'i na 9, shafi na 121