Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul Bait (As) - ABNA - ya habarta cewa: Jagoran juyin juya halin Musulunci a safiyar ranar lahadi biyo bayan harin da Isra’ila da Amurka suka kai Iran ya gana da dubban iyalan shahidan tsaro masu daraja ya kira wadannan shahidai daga cikin manyan shahidan tafarkin gaskiya. sun yi ishara da muhimmancin tsaro a dukkan al'amuran al'umma da kuma bangarori daban-daban na rayuwar jama'a, sun jaddada cewa: Iran mai karfi ce kadai za ta iya samar da tsaro da ci gaban kasa da al'umma; Don haka ya kamata Iran ta kara karfi a kowace rana a dukkan bangarorin tattalin arziki da kimiyya da siyasa da tsaro da gudanarwa.
Har ila yau Ayatullah Khamenei ya yi ishara da irin ci gaba da ayyukan muguwar gwamnatin sahyoniya wajen aikata munanan laifukan yaki a Gaza da Lebanon, inda ya kuma yi kira da a kafa kawancen kasashen duniya kan wannan muguwar gwamnati, yana mai ishara da mummunan yunkuri na gwamnatin Yahudawan Sahyuniyawa a dare biyu da suka gabata, ya kara da cewa: dangane da wanna harin sun yi kuskure suna kuma girmama wannan kuskuren da suka yi da wata manufarsu ta musamman, amma duk kuskure ne a raina shi ko a ce ai ba komai ba ne, koma ace ba shi da muhimmanci.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin yayin da yake jaddada wajabcin kawar da kuskuren da gwamnatin sahyoniyawan ta yi kan Iran ya ce: Su Sun tafka kuskure kan Iran saboda ba su san Iran da matasa da al'ummar Iran ba, kuma har yanzu ba su iya fahimtar yadda karfi, iyawa, himma, da azamar al'ummar Iran ba wanda ya zama dole mu fahimtar da su.
Ayatullah Khamenei ya nanata cewa: Tabbas wajibi ne jami'anmu su fahimci ingancin aikin da kuma aiwatar da abin da zai dace da wannan kasa da al'umma, ta yadda za su fahimci su wane ne al'ummar Iran da kuma yadda matasanta suke.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce: Wajibi ne a kiyaye wannan tunani da kwadaitarwa da shiri da jajircewa da suke cikin al'ummar Iran domin su kansu wadannan abubuwa ne masu samar da tsaro.
A ganawar da ya yi da iyalan shahidan tsaro a ranar lahadin, ya dauki hakkin shahidan tsaro da iyalansu ga al'umma a matsayin abin da ba za a iya misaltuwa a zahiri ba, sannan ya kara da cewa: Tsaro shi ne ginshikin dukkanin hanyoyin ci gaban kasa da al'umma, sannan kuma ya kara da cewa; kimar wadanda suka ceci rayukan tsaro da kuma shahidan da ake alfahari da su a wannan fage a cikin "Rundunar 'yan sanda, Basij, IRGC, sojoji da ma’aikatun tattara bayanan sirri" ya kamata a fahimci mahimmanci da kimar tsaro da ba za a iya maye gurbinsa ba.
Haka nan kuma yayin da yake ishara bias koyarwar kur'ani mai tsarki, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya dauki tsaro a matsayin wani babban ni'imar Ubangiji tare da ishara da fagagen ayyukan kariyan tsaron kasa da na al'umma, inda ya ce: a duk inda babu tsaro da masu tsaro masu kima, Shaidanci zai bayyana.
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya kira munanan ayyuka a kan iyakoki, a garuruwa, da 'yan fashi, da sata, da safarar makamai, da safarar miyagun kwayoyi, da yada jita-jita a matsayin misalan kokarin haifar da rashin tsaro, ya kuma kara da cewa: Wajibi ne kowa da kowa ya tsaya tsayin daka wajen yakar kowane irin sharri, ta yadda zai cika taken alfahari na " Ingantaccen Mai tsaro".
Yayin da yake bayani kan muhimmin abu kuma wajibi na tabbatar da tsaro da kuma kiyaye tsaro, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce: Wasu mutane a cikin wani bakon nazari da tunani suna ganin cewa kamewa daga samar da kayan aikin da ke ciwa ma'abota girman kai tuwo akwarya da suka hada da makamai masu linzami na iya samar da tsaro ga Iran. Amma a zahiri wannan mummunar fahimta tana cewa al'umma da hukumomi ne da su ci gaba da raunana kasar don a samu tsaro.
Ayatullah Khamenei ya kira ikon kasa a matsayin hanya daya tilo ta tabbatar da tsaro a kasar Iran sannan ya kara da cewa: Domin tabbatar da tsaron kasa da al'umma da ci gaban Iran, wajibi ne mu kasance masu karfi a dukkanin bangarori na tattalin arziki, kimiyya, tsaro, siyasa, gudanarwa da sauran su, sannan kuma mu kara karfi a kowace rana.
Ya yi la'akari da bala'in mamayar da a kai wa Iran a yakin duniya na farko da na biyu, duk kuwa da shelanta tsaka-tsakin kasar, ya samo asali ne daga munanan manufofin shugabanni marasa cancanta ko maciya amana, ya kuma kara da cewa: ta hanyar kau da kansu daga ainihin kayan aikin karfi sun wulakanta al’umma da kasa, sun yi ta kokarin tabbatar da tsaronsu.
Yayin da yake bayani kan wani muhimmin batu game da tsaro, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi tsokaci kan wajibcin tabbatar da tsaron tunanin mutane inda ya ce: Wadanda suke karfafa mutane ta hanyar kafofin sada zumunta da dauke da wasu abubuwan damuwa, da tsoro da shakku da yada jita-jita ko nazari da fassarar da ba daidai ba. Wadannan bias lafazin Alqur'ani ana kiransu da sunan "Murjifun" wanda Allah ya umurci Annabi da ya hukunta su idan ba su daina yin hakan ba.
Ayatullah Khamenei ya ce irin wadannan mutane suka fada shiga kuskure wajen bincike ko kuma masu son zuciya tare da yin magana ga masu mu’amala da yanar gizo, inda ya jaddada cewa: Duk abin da ya zo a cikin tunanin dan Adam bai kamata a buga shi a cikin yanar gizo ba, sai dai dole ayi la’akari da tasirinsa ga ruhiyya da yadda mutane zasu dauke shi.
Yayin da yake ishara da yawaitar maimaita batun sararin samaniyar kafofin sada zumunta a cikin makonni da kwanaki na baya-bayan nan, ya ce: Masu son yanke shawara ko quduri a sararin samaniya, ya kamata su mai da hankali lura kan yadda labaran karya ko labarin ke sa mutane tsoro da shakku.
Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: Kamar yadda jami'an kasar suke da muhimman ayyuka da suka shafi tsaron kan iyakoki da tudu da tituna da rayuwar jama'a, haka nan kuma suna da cikakken alhaki na kiyaye tsaron tunanin jama'a.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da amfani da kayan yaki na ruwan sanyi tare da kayan yaki masu zafi da makiyan al’ummu ke yi, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce: sanya yanayin tunanin al'umma ba cikin rashin aminci yana daya daga cikin abubuwan da ke cikin wannan yaki ruwan sanyin, kuma kowa ya ga yadda suke amfani da sararin samaniya don ciyar da manufofinsu gaba.
A karshen wannan bangare na jawabin nasa ya ce wa iyalan shahidan tsaro: Ku yi alfahari, kuma ku yi alfahari da shahidan ku, domin da a ce su da sauran jami'an tsaro ba su kasance ba, da an samu matsaloli masu yawa ga kasa da al’umma, don haka dukkan mutane suma su yaba wa wadannan shahidai kuma su zama iyalansu.
A wani bangare na jawabin nasa, Ayatullah Khamenei ya yi ishara da munanan laifukan gwamnatin sahyoniyawan a zirin Gaza da suka hada da shahadar kananan yara dubu goma da mata sama da dubu goma, wanda ya kasance misali na mafi girman laifuffukan yaki da kuma gazawa mai girma na gwamnatoci da kungiyoyin kasa da kasa irin su Majalisar Dinkin Duniya wajen tinkarar ayyukan ta’addanci na wannan gwamnati a Gaza da Lebanon inda yayi kakkausar suka ga hakan yana mai cewa: yaki yana da ka'idoji da dokoki da iyaka, kuma ba haka abun yake ba ace a yanayin yaki an tattake da keta haddi a yake-yake ba. Amma sai dai gungun aikata muggan laifuka da ke mulkin yankunan da suka mamaye sun murkushe duk wata doka da ke ƙarƙashin ƙafafunta.
Ayatullah Khamenei yana ganin ya zama wajibi gwamnatoci musamman gwamnatocin Musulunci su tashi tsaye wajen yakar gwamnatin masu aikata laifuka da kuma kafa kawancen kasashen duniya wajen yakar wannan gwamnatin mai aiwatar da kisa, ya kuma kara da cewa: Tsayuwa masu ba yana nufin yanke taimakon tattalin arziki ba, domin a fili yake cewa taimako mulkin mamaya yana daya daga cikin mafi muni kuma manya-manyan zunubai. Tsayuwa kuwa na nufin kafa kawancen siyasa, tattalin arziki da na duniya, idan ma akwai bukatar karfin soji wajen yakar muguwar gwamnatin da ke aikata munanan laifukan yaki.