19 Oktoba 2024 - 12:04
Sakon Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Na Iran Bayan Shahadar Jarumin Mujahid Kwamanda Yahya Sinwar.

Shi fuska ne mai walwali ta gwagwarmaya da mujahada; Ya tsaya da azama a gaban maƙiyi azzalumi dan mamaya; Ya mare makiyi cikin dabara da jarumta; Ya bar tarihin bugu kamar na 7 ga watan Oktoba da ba za a iya samun mamadin shi ba a tarihin wannan yanki; Sannan kuma ya tashi zuwa ga matakin shahidai cikin girmamawa da alfahari.

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei a cikin wani sakon da ya aike wa al'ummar musulmi da kuma matasan yankin masu kishin kasa, tare da girmama jarumi mujahidi kwamanda "Yahya Sinwar" tare da jaddada cewa: Kungiyar gwagwarmaya ba ta daina ci gaba ta hanyar shahadar fitattun mutanenta, kamar yadda ba ta tsaya da shahadar Sinwar ba in Allah Ya so. Hamas na nan da ranta kuma za ta ci gaba da rayuwa.

Nassin sakon Jagoran juyin juya halin Musulunci shi ne kamar haka;

Da sunan Allah, Mai rahama Mai jin Kai 

بسم الله الرّحمن الرّحیم

Al'ummar musulmi! Matasan yankin masu kishin kasa!

Jarumin Mujahidi kwamanda Yahya Sinwar ya sadu da abokanansa shahidai.

Shi fuska ne mai walwali ta gwagwarmaya da mujahada; Ya tsaya da azama a gaban maƙiyi azzalumi dan mamaya; Ya mare makiyi cikin dabara da jarumta; Ya bar tarihin bugu kamar na 7 ga watan Oktoba da ba za a iya samun mamadin shi ba a tarihin wannan yanki; Sannan kuma ya tashi zuwa ga matakin shahidai cikin girmamawa da alfahari.

Wane irinsa, wanda ya shafe rayuwarsa yana yakar makiya mai kwace, a karshe babu wani sakamako da dace da shi mafi cancanta face shahadar da ta. Hakika rashinsa yana da daci ga bangaren Gwagwarmaya, amma wannan gwagwarmaya ba ta gushe ba tana ci gaba dukda shahadar manyan mutane irin su Sheikh Ahmad Yasin, Fathi Shaghaghi, Rentisi da Ismail Haniyeh, kuma ba zata tsaya ba ko kadan da shahadar Sinwar. Da yaddan Allah Hamas na da rai kuma za ta ci gaba da rayuwa.

Kamar kullum, za mu ci gaba da kasancewa tare da mujahidai da masu gwagwarmaya na gaskiya; da taimakon Allah ya saka da alkhairi ya taimake ku.

Ina taya dan uwanmu Yahya Sinwar murna shahadarsa ga iyalansa, da 'yan uwansa, da dukkan masoya Jihad Faisabilullah, tare da yi ta'aziyyar ga rashinsa.

Wassalamu Ala Ibadihis Saliheen 

Sayyid Ali Khamenei

7/28/1403