Da yammacin ranar Juma’a 1 ga watan Rabi’ut Thani, 1446 (4/10/2024) ne Harkar Musulunci ta gudanar da taron addu’ar cika kwanaki bakwai da shaha-dar Sayd Nassrallah a Abuja.
Taron, wanda aka fara shi da yin addu’o’i daban-daban, a karshe Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya gabatar da takaitaccen jawabin rufewa.
A yayin jawabinsa, Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), ya bayyana Shaheed a matsayin gwarzo, kuma jajirtacce wanda ya tsaya kyam, sannan ma’abocin baiwowin hikima, iya magana, da kuma fadin gaskiya daga cikin zuciyarsa a lokacin rayuwarsa.
Yace: “Sayyid Nassrallah yana fadan abin da yake cikin zuciyarsa, wanda har makiya sun yi masa shaida akan cewa yana fadin gaskiya ne a duk abin da ya fada. Sun yarda da shi (a zantukansa), har ma suna cewa, sun fi yarda da shi fiye da shugabanninsu, domin su suna musu karya”.
Ya bayyana cewa: “Ba karamin bakin ciki muka yi ba, saboda mun rasa gwarzo daga cikin gwaraza, Sahibul Asr waz Zaman ya rasa jigo babba, don yana cikin manya-manyan ‘ya’yan Imam Khomaini (QS), kuma yana cikin wadanda muna iya ce mishi hannun dama ma na Sayyid Khamene’i (H). Wannan ba karamin barna aka yi ba.” Ya kara da cewa: “Amma a lokaci guda, bayan mun ji zafi mun yi jaje, a lokaci guda kuma mun san cewa Allah Ta’ala haka ya so. Allah Ta’ala ya so wannan bawan nasa da hutu ne. Ya yi shekara da shekaru yana fafatawa, (yanzu) sai Allah Ta’ala yace, zo kuma ka huta”.
Shaikh Zakzaky ya yi bayani dangane da yadda Shahidai suke cigaba da ayyukansu ko bayan kashe su. Yace: “Shahidi yana nan da ransa, kuma ba wai yana wani wuri ne ba, yana nan tare da mu ne yana kuma aiki, aikin da yake yi ya fi wanda zai yi inda ma yana nan.” A nan ne ya jaddada ma makiya cewa: “Ku baku sani ba, Sayyid Nasrallah yana nan, kuma ya dinga yaƙarku kenan har izuwa nasara!”.
Yace: “(Makiya) sun yi murna (da abin da suka yi), sun dauka kamar sun yi wani yunkuri ne. Ai ba gwarzantaka ba ne ka samu mutum a gida ka kashe. Gwarzantaka shi ne in kai jarumi ne, ka hadu da jarumi ku kwama, kuma wadannan ba su taba yi ba”.
Bayan bayyana yadda maqiya suka iya cimma Shahi-din, Jagora ya tabbatar musu da ba za su taba iya shafe ambatonsa ba har abada. “Kamar yadda Sayyida Zainab take fadawa Yazidu a fadarsa cewa; ‘ba za ka taba iya shafe ambatonmu ba!’ To, idan kuna iyawa yanzu, ku zo da wata na’ura ta mantar da mutane Sayyid Nasrallah!” Ya musu kule.
Yace: “Kun raya shi ne. Kun raya sunansa. Ba sunansa kawai ba, kun raya shi. Kuma shi rayayye ne har abada. Kun sa shi kuma ya shiga cikin zukatan mutane, ya shiga can cikin zuciyarsu ya zauna daram! Haka nan zai kasance kuma har izuwa karnoni masu zuwa. Kuma za ku rika ganin kaiconku ma da ma baku yi wannan aikin ba".
Shaikh Zakzaky ya jaddada alkawari ga Shahid da cewa: “Muna cewa da kai, Ya Sayyid Nasrallah, mun yi jimamin rabuwa da kai da (gangan) jikinka, kuma muna nan muna baka tabbacin cewa, insha Allahu za mu yi abin nan da ka ba da rai a kai har sai ya kai ga nasara".
Sannan ya yi kira ga ‘yan gwagwarmaya a ko ina a fadin duniya da cewa: “Sayyid Nasrallah rul-lah ya baku samfurin aiki, cewa, akan jajirce ne, a dake.” Yace: “Na ji Sayd Nasrullah a cikin kalamansa yana fadin abin da Imam Husaini ya fada ranar Karbala da yake cewa; ‘Bani ganin mutuwa a yau face sa’ada (dacewa) ne, kuma rayuwa tare da azzalumai halaka ne.’ To sai Sayyid Nasrallah yake cewa, lallai rayuwa da wadannan mutane, - don su kullum suna cewa a zauna lafiya da su ne a sasanta da su (su cigaba da zalunci) – To, wannan kam halaka ne.”
Ya kara da cewa: “A koyarwar Sayyid Hasan Nasrallah, yana cewa: ‘Mu ne magoya bayan Amirulmumimin (AS), kuma ba za mu taba kyale Palasdinu su kadai ba, ba za mu taba kyale Masjidul-Aqsa ba, muna nan daram akan goyon bayansu. Kuma wannan Alhamdulillahi ya nuna ‘yan uwantaka irin na Musulunci.
“Lokacin da nake kallon abin da ya faru ranar Talata na kai harin Iran, ga su nan hotuna daban-daban, taurari masu wutsiya suna ta sauka tar-tar-tatar-tar! “Walaqad Zayyannas Sama’ad duniya bi masabiyha waja’alnaha rujuman lis shayadiyn, wa a’atadna lahum azabas sa’ir.” Yanzu kun ga wannan ‘rujuman lish shayadin’, ga su nan suna sauka tar-tatar-tar, suna wucewa. To kuma sai ga su ‘yan Palasdinu suna ta murna.
“To bayan dai kallon (harin) da ban sha’awa, har wala yau, ganin yadda su ‘yan Palasdin abin ya faranta musu rai, har wani yana cewa; ‘da mu da ku ruhinmu daya.’ Har ya saka ni kuka. Wannan shi ne ‘yan uwantaka ta Musulunci; ana zaluntar dan uwanka, kai kuma ka taimake shi”.
Jagora ya kara jajantawa ga iyalan Shahid tare da tunatar da su cewa ya samu babban daraja ce. “Allah Ta’ala ya riskar da shi ne da kakansa Imam Husaini (AS), kuma wannan tafarkinku ne, gidanku haka ya gada, tafarkin kenan na A’immatu Ahlul baiti (AS), duk gwarzo kuma haka abin yake kasancewa da shi”.
Ya karkare da ba da uzurin cewa, mu nan ba abin da za mu iya illa nuna goyon baya ga raunanan da ake zalunta. “Mu a nan abin da za mu iya shi ne mu nuna ‘solidarity’ (goyon baya), akalla tunda ba za mu iya zuwa mu yi yaki ba, akalla yanzu ya zama mun nuna wannan ‘solidarity’ din, mun tsaya kuma da addu’o’i, musamman a sallolin dararenmu, da kuma addu’o’i Ma’asurai a yi ta yi”.
Sannan ya karkare da jajjada fatan ‘yan uwa su cigaba da karanta Du’a Ahlus Sugur, da nufin Allah Ta’ala Ya ba da nasara ga Palasdinawa da mataimakansu. Yace: “Shi ma addu’ar babban makami ne, kuma abin da za mu iya yi kenan".
@SZakzakyOffice
01/RabiuThani/1446
04/10/2024
Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)














