28 Satumba 2024 - 20:06
Afirka ta Kudu Ta Yi Allah Wadai Da Kisan Sayyid Hassan Nasrallah

Afirka ta Kudu Ta Yi Allah Wadai Da Kisan Sayyid Hassan Nasrallah

A cikin wata sanarwa da gwamnatin kasar Afirka ta Kudu ta fitar ta bayyana cewa: Jamhuriyar Afirka ta Kudu ta bayyana matukar damuwarta game da yadda ake ci gaba da samun yawaitar kashe-kashen ba bisa ka'ida ba a yankin Gabas ta Tsakiya, musamman ma kisan gillar da aka yi wa Sayyid Hasan Nasrallah da wasu shugabanni a kasar Labanon.