Murnar Tunawa Da Ranar Haihuwar Manzon Rahama Muhmmad Dan Abdullah (S) Da Jikansa Imamus Sadik As
Mun masu taya daukacin Al’ummar musulmi da wadanda ba musulmai ba dama sauran halittun duniya gaba daya murnar haihuwa shugaban Annabawa da jagorana manzanni (sawa) da haihuwar jikansa Imam Abi Abdullah Ja’afar dan Muhammad Sadik (as)
17 Ga Watan Rabi'u Auwal Ranar Farin Ciki
A yau 17 ga watan Rabi'u Auwal tayi daidai da ranar Haihuwar Fiyayyan Halitta Annabi Muhammad (S) bisa Nassin Ruwayoyin Ahlulbait (As). An haifi Manzon Allah (S) a Shekara ta 58 kafin Hijra a ranar Juma'a daidai ketowar Alfijir.
Takaitaccen Tarihin Rayuwar Annabin Rahama (sawa):
Ya Rayu da Shekaru 63 a Duniya ruwayoyi suna nuna cewa Mahifin Annabi Sayyidi Abdullahi yayi wafati lokacin Manzon Allah (S) be wuce wata Shida a cikin Mahifinyar saba! Sannan Annabi ya Rayu da Mahaifiyarsa Sayyida Amina na Shekaru 6 sannan ya Rayu da Kakansa Abdulmunaf Shekera 8 sannan kulawarsa ta koma gun Baffansa Abu Dalib inda ya Rayu dashi na tsawon Shekaru 42 daga ciki yayi Shekaru 17 a Gidansa sauran 25 yayi sune a gidan Sayyida Khadija Matarsa ta farko. Ya zauna a Makka a bayan Rasuwar Mahaifiyarsa na Shekaru 3 sannan ya koma Madina yayi Shekaru 10.
Manzon Allah ya kasance yana da shekaru 40 aka fara masa Wahayi a kogon hira a Makka.
Yayi Shahada yana da Shekaru 63 a ranar Litinin 28 ga watan Safar Shekara ta 11 bayan Hijira, Imam Ali (As) shine ya Jagoranci Jana'izarsa sannan Haraminsa na nan a Madina.
A ranar 17 ga watana Rabi’ul Auwal bisa mabanbantan shekaru aka haifi Annabin rahama (sawa) da jikansa wanda yak shine imami na shida cikin jerin imamai da Allah ya nada Annabinsa ya isar da jagorancinsu ga al’ummar duniya a bayansa:
ولد الهدى فالكائنات ضياء *** وفم الزمان تبسم وثناء
An haifi shiriya halittu sai kasance masu haske da haihuwarsa # ya zamo mutanen zamani bakunansu ya cika da murmushi da yabonsa
Dangane da haihuwar Annabin rahama (sawa) kamar yadda muka ambata a baya malaman tarihi da riwayoyinsu sun tafi kuma sun yarda akan cewa an haifi Annabi Muhammad a watana Rabu’ul Auwal ne a shekarar Giwa wanda ya kama a shekarata 570 Miladiyya bayan haihuswar Annabin Isa As.
Amma sun sami sabani akan takamaiman ranar haihuwarsa, idan muka duba ruwayar Shekh Kulaini zamu ga cewa na haifi Manzon Rahama (swa) ne a a ranar 12 ga watan Rabi’ul Auwal kuma zamu ga wanna ranar ita ce ta shahara a wajen mafi yawan mutane Ahlus sunnah.
Amma abunda yafi shahara a wajen Yan Shi’ah shine ranar 17 ga watan Rabi’ula Auwal ne aka haife shi saboda wanna sabanin ne Imam Khumain (qs) ya sanya wannan satin wato daga ranar 12 zuwa ranar 17 a matsayin satin na hadin kai inda ake gudanar da taruka na karantarwa da murna domin samun hadinkai a tsakanin Al’ummar Annabi Muhammad (sawa) saboda hadin kai shine mafi muhimmancin abu da yanzu al’ummar Musulmi suke bukata wanda kuma shine koyarwar Alkur’ani da manzon Rahama Sawa.
Annabi Muhammad (sawa) shi ne annabin Rahama Shugaba kuma jagoran Al’umma wanda Allah Ta’ala ya aiko shi zuwa ga dukkan nau’ikan halittu daya halitta’ domin shine tafarkin aminci da musulunci’ mai rike da tutar Alkur’ani’ wanda ya gagari duniya da shi a dukkan zamani da lokuta. Shi Ma’asume ni Allah ta’ala yak are shi daga dukkan aibobi da kurakurai da zunubai da dukkan abunda bai kamata ba domin baya furici akan son zuciyarsa duk abunda ya furta wahayi ne daga Allah Ta’ala:
(لا ينطق عن الهوى * إن هو إلا وحي يوحى)
Shi mai Bushara ne ga mabiyansa ga samun tsira da da shiga Aljanna da smaun jindadin duniya da Lahira da samun yarda da rahamar Ubangiji, kuma shi mai gargadi ne wanda suka ki binsa da samun tabewa da azbara Allah da wahalar duniya da lahira’ shine mai sheda akan Al’umma kuma mai kiransu da izinin Allah ubangijinsu:
( إنا أرسلناك شاهدا ومبشرا ونذيرا وداعيا الى الله بإذنه وسراجا منيرا )
Shi ne ma’abucin halaye kyawawa mafi girma wanda Allah Ta’ala bai siffanta wani Annabi da sub a gabansa da bayansa ba’ inda ya ce: Tabbasa Kai kana kan halaye mau girma.
( وإنك لعلى خلق عظيم )
Shi Ya kasance mai tsaru da tsanani akan Kafirai ne’ kuma sai tausayawa da jinkai ga Muminai: (محمد رسول الله والذين معه أشداء على الكفار رحماء بينهم).
Shi ne wanda ya kai matsayi da matakin da ba wanda ya kai zuwa matsayin tun daga na farko kuma wanda zai kai ga wannan matsayi ga na karshen:
( فدنا فتدلى فكان قاب قوسين أو أدنى )
Manzon Rahama (saw) shine Ma’abocin matsayi abin yabo wanda kowace halitta tun daga na farko har na karshe ke hankoron da shaukin kaiwa gareshi:
( وعسى أن يبعثك ربك مقاما محمودا )
Shine wanda Allah Ta
Ala ya tsarkake shi da Iyalan gidansa daga dukkan datti da kazanta domin su kasance jagororin shiriya zuwa gareshi su kasance tafarkin da halittun zasu bi domin kaiwa ga rahamarsa inda Allah Ta’ala ya ce:
(إنما يريد الله ليذهب عنكم الرجس أهل البيت ويطهركم تطهيرا)
Shine Manzon Da Allahh Ta’ala ya gwama sunansa da nasa’ kuma ya daukaka anbatonsa’ ya gwama shaidawa da Annabcinsa tare da shidawa da ubangijintakarsa inda ya ce: (ورفعنا لك ذكرك)
Shi ne wanda Allah Ta’ala zai bashi ya kara masa yayi masa tagomashi har sai yarda da aminta da gamsuwa da abunda Allah Ta’ala ya ba shi: (ولسوف يعطيك ربك فترضى)
Shi ne wanda ya ke damuwa da kuntata ga abunda ya sami ko ya cutar da Al’ummarsa da dukkan samuwarsa yana jin ciwon akan abunda suke jin ciwo akai’ kuma shine Annabin da ya ksance mai tausayawa ga Muminai tausayin da yafi na uwa garesu:
( لقد جاءكم رسول من أنفسكم عزيز عليه ما عنتم حريص عليكم بالمؤمنين رؤوف رحيم)
Da a ce za mu lissafta halaye da dabi'u da siffofin manzon Allah madaukakin sarki shugaba kuma majibincin ‘yan Adam Muhammad zababben Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi da alayensa da sun yi tsayin tsayin da babu iyaka, domin kuwa kyawawan halayensa (amincin Allah da amincin Allah su tabbata a gare shi) sun cika Alkur'ani mai girma da marubuta da masana adabi da masu tunani, kuma saboda ya shagaltar da kyawawan dabi'unsa duk wadanda suka rayu tare da shi ko suka ji labarinsa, wadanda suka saba da zamanin jahiliyya.
Imam Sadik As
Limamin Ahlul Baiti na shida, Imam Abu Abdullah Ja’afar bin Muhammad bin Ali bin Husain bin Amirul Muminin, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su, shi ya zamanto mu'ujiza madawwamiya ta duniya, kuma abin alfaharin bil'adama a tsawon zamani’ duniya ba ta taba ganin irinsa ba, kuma duniya ba ta taba jin labarin wani irinsa ba, ya hada dukkan kyawawan dabi'u, kuma ya cim ma dukkan ayyukan alheri, ya riga ya rigayi duniya da iliminsa.
Sannan a irin wannan Rana Allah ya kara saukar da Falala na Haihuwar Jikan Manzon Allah kuma Khalifansa na 6 daga cikin jerin Limaman Shirya wato Imam Jafar Assadiq (As).
Takaitaccen Taraihin Rayuwar Imam Sadik As
Tarihin Rayuwarsa a takaice: An Haife shi Ranar 17 ga watan Rabi'u Auwal Shekara ta 86 bayan Hijra a ranar Juma'a daidai lokacin ketowar Alfijir wannan Rana ce mai Albarka wanda itace Ranar da aka Haifi Fiyayyan Halitta Annabi Muhammad (S) a Madina.
Sunan Mahaifinsa Imam Muhammad Bakir (As) sunan Mahaifiyarsa Sayyida Faɗimatu wanda aka fi saninta da (Ummu Farwat).
Alkunyarsa itace: Abu Jafar ko kuma Abu Isma'il.
Dalilin da yasa ake kirasa da Assadiq (As) Suna ne da Manzon Allah (Saww) ya sanya masa yake cewa idan an haifi Ɗana Jafar Ɗan Muhammad Ɗan Aliyu Ɗan Hussaini Ɗan Aliyu Bini Abi Ɗalib ku anbacesa da Sadiq. Ya kasance tare da Kakansa da Babansa (Assajjad da Bakir) Alaihimassalam Shekarau 20 sannan ya rayu tare da Babansa bayan Rasuwar Kakansa Shekaru 16. Sannan Imamancinsa ya kasance bayan Shahadar Babansa rana ta bakwai ga watan Zul Hijja Shekaru 114 Bayan Hijra zuwa Shahadarsa a Shekara ta 148 Bayan Hijira.
Yana da Ƴaƴa kamar haka:
Isma'il, Abdullahi, Ummu Farwat, Ishaq, Faɗima, Muhammad, Abbas, Aliyu, Asma'u.
Shahadarsa: Ta kasance a 25 ga watan Shawwal Shekara ta 148 bayan Hijira sannan Haraminsa na nan a Madina cikin Maƙabartar Baƙi.
Ta yaya za mu yi magana game da Imam Sadik, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ma’ana iliminsa, tunda shi ne wanda ya cika duniya da saninsa da iliminsa – kamar yadda Al-Jahiz yake cewa – ko kuma ma ace mun yi magana game da mazhabarsa, wanda tarihi a zamaninsa da tsararrakinsa ba su shaida irinta ba? Idan ba a manta ba makaranta ce mai dalibai sama da dubu hudu da ake koyar da fikihu, hadisi, tafsiri, Akhlaq, falsafa, falaki, likitanci, chemistry, da sauran ilimomi da fasaha.
Sauran abubuwan da suka shafi rayuwarsa, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ba su gaza a fagen ilimi ba. fagagen rayuwa, a yayin da muke samun wasu wadanda idan suka kware a abu daya, sai su gaza ga wasu, zaka ga idan mutum ya zamo malami ya yi nisa da jarumtaka, idan kuma mutum aka samu ya zamao jarimi to zaka ga yayi nesa zuhudu da tsoron Allah, amma su iyalan gidan gidan Annabata sun tara komai sun tara kyawawan halaye da darajoji, kuma sun gabaci mutane a cikin kowane aiki mai kyau da kyawawa sun kasance tsira da amincin Allah su tabbata a gare su, su ne mafifitan mutane a kowane hali suna da mafi fadi a cikin halaye, mafi girman ibada, mafi girman masu yin zakka, mafi alherin su ga haquri, mafi tsarkin su a cikin ayyuka, kuma mafi alherin su. Su ne fitattun mutane a duniya, kuma dukkansu sun fi kowa fifiko da rigaye.
An haifi Imam Sadik, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a ranar Juma’a ko ranar litinin, daidai ketowar Aifijir, kwana goma sha uku da suka rage a watan Rabi’ul Awwal na shekara tamanin da uku, ko shekara ta tamanin da shida, kuma an bawa Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa labarin zuwansa sai ya ce: “Idan aka haifi dana Ja’afar bin Muhammad bin Ali bin Husain ku sanya masa As-Sadik, domin na biyar daga cikin ‘ya’yansa sunansa Ja’afar ne zai riya cewa shi Imami ne bisa karya da kagewa Allah ta hakan zai zamo Ja’afar makaryaci a wajen Allah... Abin da aka sani ya shahara dangane da ranar haihuwarsa a wajen malaman fikihu shi ne, an haife shi ne a ranar sha bakwai ga Rabi’ul Awwal.
Muna mika sakon taya murna da fatan alheri zuwa ga Jagowa Majibincin Allah kuma Jagoran Zamani, Muhammad binil-Hasan Al-Mahdi, zuwa ga manyan maraji’ai, da daukacin musulmin gabas da yammacin duniya a maulidin manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa da kuma jikansa Imam Ja’afarus-Sadik, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
Salati da aminci su tabbata ga Muhammadu da alayensa
Allah Ya Kai Ladan Wannan Bahasin Zuwa Ga Ruhin Sheikh Adamu Tsoho Jos Ya Daukaka Darajarsa Sannan Mu Kuma Allah Ya Tabbata Damu Akan Tafarkin Iyalan Gidan Annabi (S)