Kamfanin dillancin labaran kasa
da kasa na Ahlul-Baiti As - ABNA - ya kawo maku bayani dangane da ladubban bayan
anci abinci inda ya fara da cewa: A Musulunci akwai ladubba da nasihohi a kan
abubuwa da yawa, wanda a cikin wannan bayanin mun yi ishara da maganganun Imamai
da ladubba da shawarwarin Musulunci a bayan cin abinci.
Yin Addu’a: Batu na farko shine a yi addu'a bayan an gama cin abinci. Imam Sadik (a.s.) yana cewa: Idan kun gama cin abinci sai ku ce: « الْحَمْدُ لِلَّهِ الَّذِي يُطْعِمُ وَ لا يُطْعَمُ» "Godiya ta tabbata ga Allah wanda yake ciyarwa amma shi ba’a ciyar da shi abinci".
Zama A Gefen Shinfidar Abinci: wani ladabin bayan cin abinci shi ne kada a tashi daga gefen teburin har sai an nade shimfidar abincin gaba daya, domin Annabi (SAW) ya hana hakan. Ya askance yana jira har sai an kwashe kayan abincin gaba daya.
Cinye Abincin Da Ya Fadi Akan Shinfidar Abincin: Har ila yau dangane da abincin da yake zuba kan tebur Annabi (SAWA) kasance la’akari da hakan yana cewa: “Duk wanda ya cinye abincin da ya zubar kan tebur a yayin da yana ci abinci to zai wadatu da arziqi matukar yana raye. Wannan shi ne koyarwa ta uku na Musulunci a cikin ladubban bayan an ci abinci, kuma a kan haka ma Manzon Allah (SAW) ya ce a cikin wani hadisi cewa: “Allah Ya haramtawa wutar Jahannama ga jikin wanda ya tattara abincin da ke kan shinfidar abinci ya cinye".
Wankewa Tare Da Sakace Hakora: Batu na hudu shine Annabi (SAWA) ya koyarwa da a rika wanke hakora bayan an ci abinci, domin wanke hakora na sanya kamshi da lafiyar bakin. Hakazalika, ya ce: “Bayan kun ci abinci ku sakace hakuranku domin bbau abu da mala’ikun Allah suka fi ga bawa sama da sauran abincin da saura tsakanin haƙoran bawa”.
Sayyidina Ali (a.s) ya kuma yi umarni bayan an sakace hakora yana cewa: "Ku zuba ruwa sau uku ku kuskure sannan ku zubar da shi daga bakinku".
Godiya Ga Allah A Karshen Cin Abinci
A Musulunci ya zo cewa: «اذا اکلت او شربت فقل: الحمدلله» "Idan ka ci abinci to ka ce: Alhamdulillah.
Koyarwar A’imma (AS) bayan cin abinci:
Lasa Gishiri A Farkon Da Kuma Ƙarshen Abincin
A cikin wasu ruwayoyin, ana so ayi anfani da Ruwan Kal maimakon gishiri a ƙarshen cin abinci. Ɗaya daga cikin abubuwan da Ruwan Kal shine yak e anfanarwa shi ne ƙwakwalwa da hankali. Akwai abubuwan anfani da yawa na gishiri a cikin ruwayoyin, wadanda suka hada da rigakafi daga kuturta, majibi, ciwon makogwaro, ciwon hakori, da ciwon ciki. Don haka duka biyun suna da amfani kuma kowane ɗayan ana iya ɗauka ayi anfani da shi.
Wanke Hannu Bayan Cin Abinci
Manzon Allah (S.A.W) yana cewa: Wanka (hannaye) gabanin cin abinci da bayan cin abinci waraka ne ga jiki kuma mabubbugar albarka a yini.
Shafa Fuska Da Addu'a Bayan Wanke Hannu
Annabi Muhammad (S.A.W) yana cewa: Idan za ku wanke hannaye bayan cin abinci, kafin ku busar da su da kyalle, to ku shafa fuska da idanunku, sannan ku ce:
"Ya Allah! Ina rokonka kyakkyawa da abota, kuma ina neman tsarinka daga kiyayya da qeta".
Imam Sadik (a.s.) yana cewa: Idan za ku wanke hannaye bayan cin abinci, to, ku sha idanuwanku da sauran ruwan da ya rage, domin shi ne kariya daga ciwon ido.
Kwanciya Ta Bayanka Bayan Cin Abinci
An ambaci cewa bayan ya ci abinci ana so mutum ya kwanta a bayansa (ya huta) ya dora kafarsa ta dama a kan kafarsa ta hagu.
Imam Sadik (AS) yana cewa: Kwanciya bayan cin abinci yana sanya jiki yayi kiba. Yana narkar da abinci kuma yana fitar da radadin daga jikin mutum.
Imam Riza (AS) yana cewa: Duk lokacin da za ka ci wani abu, to ka kwanta a bayanka, ka dora kafar dama a kafar hagu.
Kuma A Ƙarshe, Kaucewa Da Kauracewa Barci Nan Da Nan Bayan Cin Abinci!