19 Yuli 2024 - 15:22
An Kai Hari Da Jirgin Sama Mara Matuki A Tsakiyar Babban Birnin Yahudawan Sahyoniya/ Ya Kashe 1 Ya Jikkata Wasu 8 + Bidiyo

An kashe wani dan sahayoniya a wani harin da jirgin mara matuki ya kai a Tel Aviv.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na kasa da kasa na Ahlul Bayt (AS) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: majiyoyin yada labarai sun bayar da rahoton cewa, an kai wani hari da jirgin yaki marasa matuka a tsakiyar birnin Tel Aviv fadar mulkin gwamnatin sahyoniyawan.

A cewar rahoton, wani gini da ke kan titin "Ben Yehuda" da ke tsakiyar birnin Tel Aviv, kusa da ofishin jakadancin Amirka da ke wannan birnin, an kai masa hari da wani jirgin sama mara matuki, inda ya kashe yahudawan sahyoniya guda 1 tare da jikkata wasu 8.

Kafofin yada labaran gwamnatin Sahayoniya, sun ambato daga majiyoyin tsaro, inda suka bayar da rahoton cewa, wani babban jirgi maras matuki ya nufo birnin Tel Aviv daga fuskacin teku, kuma ba a san yadda ya bi takan dukkan matakan tsaro ba tare da kai hari kan wani gini a birnin Tel Aviv.

A halin da ake ciki kuma tashar 13 ta gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta sanar da cewa jirgin mara matuki mai saukar ungulu yana tafiya ne da shawagi a cikin matsakaicin tashi, don haka tsarin tsaro na sojojin mamaya ba su yi nasarar dakile shi ba.

Yaman tana da hannu kan harin da aka kai a babban birnin yahudawan sahyoniya

A gefe guda kuma, tashar Al-Masira ta bayar da rahoton cewa, nan da 'yan sa'o'i kadan ne sojojin kasar Yemen za su kaddamar da wani samame na musamman ta hanyar fitar da sanarwa.

Yahya Saree, kakakin rundunar sojin Yaman, shi ma ya sanar da wannan bayani cewa, yana da cikakken bayani kan harin da aka kai Tel Aviv.