Kamfanin dillancin labarai na kasa da kasa na Ahul
Bait (As) – ABNA – ya habarta maku cewa: jaridar “Wall Street Journal” ta kasar
Amurka, daya daga cikin jaridun da ke da matukar muhimmanci da tasiri a fannin
tattalin arziki da siyasa a duniya, ta rubuta cewa: Iran ta kalubalanci Amurkan
ta samun iko a fagen kasa da kasa. Kuma duk da matsin lamba na takunkuman shekaru da yawa daga kasashen yamma gareta, yanzu Tehran ta zama barazana da muradun Amurka.
An bayyana a cikin wannan rahoton cewa: Wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasar Iran zai gaji ikon karfin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, wanda hakan ke nuna irin tasirin da Iran ke da shi a fagen kasa da kasa idan aka kwatanta da baya. Bisa rawar da jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya taka, kasar Iran ta samu nasarar kawar da matsin lambar takunkumai na dogon lokaci da Amurka tai ta faman sanya ma ta, tare da kawar da kanta bayan da ta juya ta koma kulla alakar dangantaka da yankin gabashin duniya inda ta karfafa dangantakarta da kasashen Sin da Rasha, kuma a lokaci guda ta ƙara matakin adawarta da Washington.
Jaridar Wall Street Journal ta yi imanin cewa, tun bayan gazawar tsohon shugaban kasar Amurka Jimmy Carter wajen shawo kan Iran, wannan kasa ba ta zamo wani makami a hannun diflomasiyyar kasashen yammacin duniya ba, haka kuma takunkumai ba su yi tasiri ba wajen mayar da Tehran saniyar ware ba a duniya.