8 Yuni 2024 - 13:52
Bayanin Rufe Taron Kungiyar D8 A Istanbul Ya Gudana Akan Falasɗinu Da Neman Samun Yan Cinta

An gudanar da wani taro na musamman na ministocin harkokin wajen kasashen musulmi 8 masu tasowa a birnin Istanbul kan batun Gaza, kuma daga karshen bayaninta ta bayyana cewa: Muna bukatar tsagaita bude wuta cikin gaggawa, na dindindin ba tare da sharadi ba a Gaza da kuma kawo karshen hare-haren da Isra'ila ke kai wa al'ummar Palastinu a Gaza.

Har ila yau, an bayyana a cikin wannan sanarwa cewa: Muna jaddada cikakken goyon bayanmu kan kasancewar Falasdinu a matsayin ƙasa a Majalisar Dinkin Duniya da kuma goyon bayan da kasashen D8 ke ba wa al'ummar Palastinu.