Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: bisa nakaltowa daga kamfanin dillancin labarai na Aljazira cewa Ofishin Yada Labarai na Gwamnati a Gaza ya ce An sake gano kabarin bai daya a karo na uku a cikin rukunin gine-ginen asibitin Shifa kuma an tono shahidai 49 daga cikinsu.
