Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (AS) - ABNA - ya habarta cewa, an gudanar da shagulgulan Taron bikin Taklifin 'yan matan tare da halartar Ayatullah Ramazani, babban shugaban majalisar Ahlul-Bait (AS) ta duniya a rukunin "Vipaz" a kasar Tanzaniya. Wannan biki da aka gudanar a karon farko tare da halartar 'yan matan Shi'a da Sunna, tare da rera wake na addini da na juyin juya hali irin su "Salaam Farmandeh" hakan ya tabbatar da kyakkyawan sha'awar matasan kasar ga tsaftataccen addinin Musulunci.