18 Mayu 2022 - 19:29
Yan Majalisar Kasar Aljeriya Sun Bukaci A Haramta Kulla Huldar Diplomasiya Da Isra’ila

Rahotanni sun bayyana cewa yan majalisun Kasar Aljeria sun gabatar da Daftarin kuduri ga majalisar dokokin kasar, na neman amincewa da dokar da za ta haramata kulla duk wata huldar Diplomaiya da Isra’ila da kuma haramta yin tafiya zuwa isra’la ko wata dangantaka ta kai tsaye ko bayan fage da jami’an gwamnatin Isra’ila.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Yoused Ajesa dan majalisar dokokin kasar Aljeria da ya fito daga jam’iyar movement of society for peace ya fadi cewa suna fatan wasu yan majalisun da za su hade da su wajen ganin kudurin ya samu karbuwa, sai dai rashin samun gamsaishiyar Amsa yasa aka gabatar da kudurin a halin yanzu.

Kudurin ya kunshi abubuwa guda 7 da suka hada da mayar da kulla hulda da isra’ila a matsayin babban laifi da kuma haramta yin wata dangantaka da wani jami’in gwamnatin Isra’ila ko kuma yin wata tafiya zuwa hamaramtacciyar kasar.

Kasar Aljeria tana daya daga cikin kasahen larabawa da suka ci gaba da rike nuna goyon bayansu ga Falasdinu da kuma adawa da isra’ila , minisatan harkokin wajen kasar Matane Lamamra ya sha nanata cewa kasashen larabawa su nun goyon bayansu ga alummar falasdinu mai makon nuna goyon baya ga gwamnatin mamaya ta Isra’ila.

342/