15 Mayu 2022 - 16:29
​Lebanon: An Fara Zaben ‘Yan Majalisar Dokokin Kasar Lebanon A Safiyar Yau Lahadi

An bude rumfunan zabe a dukkan shiyoyi 15 na kasar Lebanon don zaben ‘yan majalisar dokokin kasar mai kujeru 128.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Tashar talabijin ta Almayadeen TV ta bayyana cewa ana gudanar da zabubbukan yan majalisar dokokin kasar Lebanon a safiyar yau Lahadi ne cikin shirin ko ta kwana na jami’an tsaro a duk fadin kasar don tabbatar da cewa an gudanar da zaben cikin amince da zaman lafiya.

‘Yan takara da jam’iyyu daban daban 718 ne suke takarar shiga majalisar dokokin kasar mai kujeru 128. Sannan wannan shi ne zaben yan majalisar dokokin kasar tun shekara ta 2018, sannan bayan rugurgujewar tattalin arzikin kasar a cikin yan shekaru da suka gabata.

Kafin haka dai shugaban kungiyar Hizbullah wacce take gwagwarmaya da HKI da makamai Sayyid Hassan Nasarallah ya bayyana cewa zaben na yai zai fayya ce matsayin wadanda suke adawa da kungiyar, sakamakon zaben zai kunyata su saboda mutanen sun ji dadin zaman lafiya da suka dandana bayan shan kayen da HKI ta yi shekaru 15 da suka gabata.

342/