8 Afirilu 2022 - 20:13
Turkiyya Ta Mikawa Saudiyya Ragamar Shari’ar Kisan Khashoggi

Turkiyya ta sanar da mikawa mahukuntan Saudiyya ragamar gudanar da shari’ar kisan dan jaridan nan Jamal Khashoggi.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Alkalin kotun Istanbul ya bayyana a wannan Alhamis cewa an rufe wannan shari’ar, kuma za’a mika kundin takardun shari’ar ga Saudiyya, kamar yadda mai shigar da kara na gwamnatin Turkiyya ya bukata na rufe sharia’ar da kuma mika ta ga Saudiyya.

‘Yan Saudiyya 26 ne ake ake wa shari’ar a Turkiyya kan kisan gillan dan jaridan a cikin karamin ofishin jakadancin Saudiyya da ke Santambul a cikin shekarar 2018, wanda kuma har yanzu ba’a ga gawarsa ba.

Masana na ganin wannan matakin bai rasa nasaba da yadda Turkiyya ke son kyautata alakarta da Saudiyya a baya baya nan, saidai Turkiyya na mai cewa ta yi hakan ne saboda bata samun hadin kai daga mahukuntan Saudiyyar game da shari’ar.

Saidai tuni amaryar dan jaridar ta sanar da cewa za ta daukaka kara kan wannan hukunci.

342/