Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Sanarwar ta ci gaba da cewa; “ Mafi karancin abinda kungiyar jama’atu za ta iya fada shi ne, tana bakin ciki da kuma karancin kalmomin da za ta yi amfani da su domin bayyana abinda ya faru na harin da aka kai wa jirgin kasa a ranar 28 ga watan Maris na 2022.”
Har ila yau sanarwar ta ce; Harin wanda an tsara shi ne da kyau,abu ne na yin Allah wadai da shi kuma abin kyama ga duk wani ma’abocin hankali.
Wani sashe na sanarwar ya ce; “ A zahiri ayyukan na keta da hatsaniya, da kisa da kone-kone da suke faruwa a tsakiyar mutane, ko akan hanyoyi sun riga sun zama jiki ta yadda ba ma jin zafinsu.”
342/