31 Maris 2022 - 17:18
Iran Tace “ Gwamnatin Sahyuniya ce Babbar Matsalar Musulmin Duniya

A ranar lahadi da ta gabata ce ministocin harkokin wajen kasashen larabawa guda 4 na masar hadaddiyar daular larabwa Baharain da Moroko ne ne suka halarci wani taro da Isra’ila ta shirya tare da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Amir Abdollahiyan yace halartar wannan taron a yankin Negev na falasdinu da ta mamaye cin amanar Alummar falasdinu ne. yace abin bakinciki yadda wasu kasashen yankin ke kulla huldar da Isra’aila duk da gabar da takun sake da take yi da kasashen musulmi game da masallacin kudus mai tsarki da kuma yankunan falasdinawa da ta mamaye

Ministan ya harkokin wajen na Iran ya furta hakan ne a ganawarsa da mataimakin Fira ministan kasar Qatar a gefen taro karo na 3 na kasashen dake makwabtaka da kasar Afghanistan a yammacin kasar China, kuma dukkan bangarorin biyu sun jaddada game da muhimmacin karfafa dangantakar Tattalin arziki da sauran bangarori dake tsakanin kasashen biyu.

342/