Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Associated Press ya bayar da rahoton cewa, rahoton ya bayyana matsalar ‘yan gudun hijira da hare-haren kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi da na ‘yan ta’adda da kuma kalaman kyama da wasu kafafen yada labarai ke yi, a matsayin muhimman abubuwan da suka kara haifar da yaduwar kyamar Musulunci a duniya a shekara ta 2021.
Rahoton ya kuma bayyana cewa nahiyar Turai ce ta farko a wajen yawan masu kyamar addinin Islama, sai kuma Asiya da Arewacin Amurka.
Rahoton ya ce kasashen Faransa da Birtaniyya ne suka fi yawan masu kyamar addinin Islama, yayin da a Indiya da Sri Lanka, kyamar addinin Islama ke karuwa saboda takun-saka tsakanin mabiya addinin Buddah da musuulmin Rohingya.
Rahoton ya nuna cewa hare-haren masu tsatsauran ra'ayi kan musulmi sun ragu a Amurka.
Haka nan kuma sassan duniya daban-daban sun shaida karuwar kyamar Islama yayin barkewar annobar Covid-19, Wasu shafukan yanar gizo da shafukan sada zumunta sun zargi musulmi da yada cutar, suna masu cewa wasu na da alaka da yada cutar da gangan saboda sallar jam'i.
Rahoton ya ce hare-haren da ake kai wa masallatai da keta alfarmar kur’ani mai tsarki da cin mutunci a shafukan sada zumunta ko cin mutuncin Manzon Allah (SAW) ya ragu a shekarar 2021.
Hakanan adawar sanya hijabi ko burqa ya ragu tsakanin 2020 zuwa 2021; Kasashen Faransa da Switzerland da Indiya da Austria, na daga cikin kasashen da suka haramta sanya hijabi a ofisoshin gwamnati da jami'o'i da makarantu. Sauran kasashe irin su Belgium, Norway, Netherlands, Jamus, Spain, Italiya, Denmark, Bulgaria, Latvia, Kosovo da Sri Lanka, sun dauki matakan hana sanya hijabin nea wurare na bai daya.
342/