Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Kakakin rundunar sojojin Najeriyar, Bernard Onyeuko, ya fadawa kafafen yada labarai cewa a cikin makonni biyun da suka gabata, sojojin Najeriya sun kaddamar da gagarumin shirin yaki da kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi na "Boko Haram" da “kungiya mai fafutukar kafa daular musulunci a yammacin Afrika wato ISWAP” a shiyyar arewacin kasar.
Sojojin sun yi nasarar kwace makamai masu tarin yawa da kayan yaki a lokutan kaddamar da farmakin, a cewar sanarwar.
342/