19 Faburairu 2022 - 13:41
​Iran Ta Mayar Da Martani Kan Wasu Rahotanin Da aka Murgudasu Dangane Da Tattaunawar Vienna

Kakakin Ma’aikatar harkokin wajen kasar iran da yake mayar da martani mai zafi game da rahotanni karya da aka wallafa kan tattaunawar da ake yi na cire mata takunkumi a birnin Vianna, yace yarjejeniyar karshe da za’a fitar game da batun dawowar Amurka cikin yarjejeniyar zai sha banban sosai da rahotanni da aka yada a hanzu.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A baya bayan nan ne kamfanin dillacin labaran Reuters ya wallafa labarin dake ikirarin cewa ya samu falle 20 na bayanai da suka kunshi tattaunawar Vianna da kuma irin matakan da kowane bangare zai taka wajen aiwatar da yarjejeniyar.

Saed Khatibzade ya fadi haka ne a shafinsa na twitter, ya kuma kara da cewa yada rahotannin da aka murguda yana da hadari sosai, yace za’a ci gaba da fidda rahotannin da aka murguda sosai musamman ganin aski yazo gaban goshi a tattaunawar ta Vienna don cire mata takunkumi

Tattaunawar vienna zagaye na 8 tana mayar da hankali ne wajen ganin an cirewa iran takunkumin zalunci da Amurka ta kakaba mata, kuma an koma tattaunawar ne a ranar 8 ga watan Fabarairu bayan takaitacen hutu da ka yi.

342/