17 Faburairu 2022 - 14:02
Bakiry: Muna Gab Da Cimma Yarjejeniya A Birnin Vienna

Mataimakin ministan harkokin wajen Iran, wanda yake jagorantar tawagar kasar a tattaunawar Nukiliya, Ali BAkiry Kani ne ya ce; Lokaci ya yi da dukkanin bangarorin da suke cikin tattaunawar za su yanke hukunci na karshe, sannan kuma ya kara da cewa; An kusa kulla yarjejeniyar karshe.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Bakiry wanda ya wallafa sako a shafinsa na Twitter ya kara da cewa; Bayan tsawon makwanni na tattaunawa, mun kusa cimma yarjejeniya a kowane lokaci daga yanzu, sai dai ba za a kulla yarjejeniya akan wani bangare ba, matukar ba a yarda da dukkan batutuwan da aka bijiro da su ba.

Tun a ranar 27 ga watan Disamba ne dai aka bude tattaunawa karo na 8 sai dai an rika samun tsaiko, inda wakilan kasashe su ka rika komawa gida domin yin shawarwari da gwanatocinsu.

342/