Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - kasar Iran ya kara da cewa da farko maganin ya sami amincewar hukumar abinci da magunguna na cikin gina a nan Iran sannan a halin yanzu yana cikin marhala ta amincewar hukumar lafiya ta duniya wato WHO.
Kamfanin Tak-Gene na kasar Iran wanda ya samar da maganin mai suna 'BioDiab' ya ce maganin zai taimaka wajen nika abinci a cikin ciki da kuma hana irin cutarwar da shuga takewa hanta da kuma wasu gabban cikin mutum a cikin ciki.
Labarin ya kara da cewa kamfanin ya dau shekaru yana aikin a kan wannan maganin kafin ya kai ga marhalar da yake ciki a yanzu.
342/