10 Janairu 2022 - 14:59
An Zabi Mohammad Al-Halbousi A Matsayin Kakakin Majalisar Kasar Iraki A Karo Na Biyu

A jiya ne majalisar dokokin kasar Iraki ta yi zamanta na farko tun bayan da aka gudanar da zaben yan majalisu a fadin kasar a watan oktoban da ya gabata, kuma daga karshe an zabi Al-halbousi a matsayin sabon shugaban majalisar a karo na biyu,

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Da farko an yi takaddama tsakanin jam’iyun siyasar kasar inda kowa wanne bangare ke ikirarin shi ne ke da rinjaye a majalisar , kafin daga bisani shugaban majalisar na riko ya dage zaman, bayan da aka dawo aka kada kuri’a da ya kai ga zaben al-halbousi a matsayin sabon kakakin majalisar dokokin kasar

Bisa kundin tsarin mulkin kasar Majalisar na da wa’addin kwanaki 30 bayan zabe ta zabi sabon shugaban kasar wanda zai umarci bangare mafi rinjaye a majalisar ya kafa sabuwar gwamnati.

342/