30 Disamba 2021 - 15:26
Sudan: ‘Yan Bindiga Sun Sace Amincen Hukumar Abinci Ta Duniya OCHA a kasar Sudan

Hukumar OCHA ta abinci ta kuma MDD a kasar Sudan ta bada labarin cewa ‘yan bindiga sun shiga rumbunan ajiyar abincinta a garin El-Fasha na yankin Darfud ta Arewa inda suka sace abincin da ta ajiye a cikin rumbunar ajiyarta.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Jaridar Sudan Tribune ta nakalto majiyar hukumar tana fadar haka a a jiya Laraba ta kuma kara da cewa, ‘yan bindigan sun kai hari kan rumbun ajiyar abincin nata ne a ranar 28 ga watan Decemba da muke ciki, kuma kwanaki 4 kacal kafin haka sun kai wani hari irinsa a tsohon sansanin sojojin UNAMIS inda hukumar take ajiye wasu abincin nata suka sace shi.

Labarin ya kammala da cewa hukumar ta OCHA ta ce tana da abinci mai yawan ton 1,900 a rumbun ajiyarta na El-Fasha, amma bata bayyana yawan abincin da yan bindigan suka sake ba.

342/