11 Disamba 2021 - 13:42
​Senegal: An Sake Farfado Da Kujerar Firai Minister A Kasar

Majalisar dokokin kasar Senegal ta sake raya kujerar firai ministan bayan an shafe shi na shekaru biyu. Jaridar Lemon ta kasar Faransa ta bayyana cewa a jiya jumma’a ce majalisar dokokin kasar ta Snegal a birnin Daka ta amince ta sake farfado na kujerar firai minista bayan da aka shafe shi a shekara ta 2019 bayan da Maky Sall ya dare kan kujerar shugabancin kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - Labarin ya kara da cewa yan majalisa 92 suka amince da kudurin sake raya kujerar, sai wakilai biyu da suka ki amincewa, da kuma wasu 8 da suka ki kada kuri’unsu.

Bayan amincewa da sake raya kujerar, shugaban kasar ta Senegal ya bayyana amincewarsa da wannan matakin, sannan ya kara da cewa kasar Senegal zata karbi shugabancin kungiyar tarayyar Afirka nan ba da dadewa ba, don haka ayyukansa zasu yi yawa, don haka a cikin watan Jeneru na shekara ta 2022, bayan zabubbuka za’a nada sabon firai minister. Sannan za’a mayarwa shugaban kasa ikonsa na rusa majalisar dokokin kasar idan ya gay a dace.

342/