5 Disamba 2021 - 16:21
Sojojin Sudan Zasu Bar Siyasa Bayan Zaben 2023, Inji Janar Al-Burhan

Babban hafsan sojin Sudan kana shugaban mulkin rikon kwarya na kasar, Janar Abdel Fattah al-Burhan ya bayyana cewa sojojin kasar zasu bar harkokin siyasa bayan zaben da ake sa gudanarwa a 2023.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA- Janar Al-Burhan, wanda ke bayyana hakan a wata hira da kamfanin dilancin labaren Reuters, ranar Asabar, ya ce, idan aka zabi wata gwamnati, bana tsamannin sojoji ko wasu jami’an tsaro zasu shiga harkokin siyasa.

Game da batun kashe masu zanga zangar adawa da juyin mulkin soji, janar al’Burhan, ya ce, ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano suwa ke da hannu kuma a hukunta wadanda suka aikata laifi, saidai ya kara da cewa sojojin sun murkushe masu zanga zagar da suke wuce gona da iri ne.

Juyin mulkin da sojojin Sudan sukayi na kawo karshen yarjejeniyar da aka cimma tsakanin sojoji da fararen hula bayan kifar da mulkin Omar Al-bashir, ya janyo kakkausan martani daga kasashen duniya, musamman kan cafke jami’an gwamnatin da kuma amfani da karfi kan masu zanga zanga da juyin mulkin, inda rahotanni ke cewa an kashe mutane akalla 44 da kuma raunata da dama, kuma dayewa daga cikinsu ta harbin bindiga.

342/