2 Disamba 2021 - 12:53
Hukumar NCDC: Rigakafin Korana Da Ake Yi Na Samar Da Kariya Daga Sabuwar Cutar Omicron

Shugaban hukumar dakile yaduwar cututtuka ta Kasa NCDC Ifedayo Adetifa ya hori ‘yan Najeriya da su yi watsi da jita-jitar da ake yadawa na cewa wai maganin rigakafi baya ba wa mutane kariya daga kamuwa da cutar korona samfurin Omicron mai saurin kisa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Har Ila yau Adetifa ya ce har yanzu yin allurar rigakafin Covid -19 na daga cikin matakan samun kariya daga kamuwa daga cutar.

“Idan maganin rigakafi na samar wa mutum kariyar Kashi 90% daga kamuwa da sumfurin Delta maganin rigakafin zai iya samar wa mutum kariyar Kashi 80% daga kamuwa da samfarin Omicron.

Hukumar ta ce har yanzu dai babu wani rahoton wannan sabuwar cuta ta yi kisa a Najeriya, amma fa an gano wasu mutane dake kamu da ita a kasar .

Tuni hukumat ta bukaci Mahukumta a Najeriya da su sanya ido sosai ga fasinjojin dake shigowa kasar domin hanya sabuwar Cutar ta Omicron mai firgita duniya

342/