Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Labarin ya ci gaba da cewa tuni aka kwashe kayayyaki a majalalisar da kuma gawawwakin mutane biyun da suka rasa rayukansu. Ya zuwa yanzu dai babu wani karin haske game da musabbabin fashewar.
Sojojin kasar Uganda suna yaki da kungiyar Alka’ida dake da alaka da kungiayr Al-shabab ta kasar Somaliya a wani bangaren na ayyukan samar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika.
Kungiyar Al’shabab ta kai hare-hare a kasar Unganda, a karon farko a watan da ya gabata. Alshabab mai ikrarin jihadi da kuma kira zuwa kafa kasar Musulunci ce ta dauki alhakin wani hari da aka kai a kasar Uganda a baya.
342/