13 Nuwamba 2021 - 16:27
Iraki: Runsunar Hashdushabi Ta Fara Aikin Tabbatar Da Tsaro A Lardin Salahuddin

Dakaron sa kai na kasar Iraki wadanda ake kira Hashdushaabi sun fara wani shirin tabbatar da tsaro na musamman a lardin Salahuddin na kasar a jiya Alhamsi.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : ya bayyana cewa wannan aikin tabbatar da tsaro zakulo ragowar mayakan kungiyar Daesh a wannan lardin, da kuma tabbatar da cewa babu wani dan kungiyar ‘yan ta’adda da ya rage a cikin lardin.

Har’ila yau labarin ya kara da cewa dakarun da suke wannan aikin sun hada da runduna ta Hashdu da ke Kirkuk da gabacin kogin Furaat.

A shekara ta 2017 ne sojojin kasar Iraki tare da taimakon Hasdu suka kawo karshen mamayar da mayakan kungiyar yan ta’adda ta Daesh suka yiwa arewacin kasar Iraki. Amma har yanzun akwai ragowar yayan wannan kungiyar nan da can da suke son hargitsa harkokin tsaro na kasar Iraki a lardunan Baddaza, Diyala, Ninawa, Salahuddin da Ambar.

342/