8 Nuwamba 2021 - 12:07
​Jam’iyun Siyasa A Mali Sun Bukaci Gwamnati Ta Mutunta Jadawalin Mika Mulki

Gamayyar jam’iyun siyasar kasar mali sun gudanar da wani taro a birnin Bamako kuma sun yi kira ga jagororin juyin mulki dake rike da gwamnti da su cika alkawari wajen shirya zaben shugaban kasa a shekara mai zuwa domin komawa kan turbar demukuradiya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Su dai jamiyun suna zargin gwamnatin kasar da kokarin jan kafa a kalandar da aka tsara ta jadawalin mika mulki a kasar, da za’ayi a watan Fabarerun shekara ta 2022

Idan ana iya tunawa a baya bayan nan ne kungiyar tarayyar Afrika da ta bunkasa tattalin arzikin Afrika Ecowas suka aike da tawaga zuwa birnin Bamako domin matsin lamba kan gwamnatin kasar da ta yi aiki da Alkawarin da ta dauka na shirya zabe a lokacin da aka tsara. Sai dai fira ministan Choguel Miaga ya sansar da cewa akwai yi yuwar a samu jinkiri na yan watanni kafin mika mulki.

A yau ne shuwagabannin kasashen Afrika suke gudanar da taro kan halin da kasashen Mali da Guinea ke ciki domin gano bakin zaren warware matsalar kasashen da taki ci taki cinyewa.

342/