7 Nuwamba 2021 - 11:51
Libiya Ta Kori Ministar Harkokin Wajenta, Najla Al-Mangoush

Majalisar shugabancin Libiya, ta sanar da korar ministar harkokin wajen kasar Najla Al-Mangoush, tare da haramta mata fita daga kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Ba’a dai bayyana takamaimai mi ake zarginta da aikatawa ba, amma kafofin yada labaren kasar da dama suka rawaito cewa an kore ta ne saboda sabawa ka’idodin aiki.

Saidai wata kafa dake da kusanci da janar Khalifa Haftar dake da karfin fada a ji a gabashin kasar, ta ce an kori ministar ce saboda ta dauki wasu matakai na siyasa da suka shafi harkokin ketare ba tare da tuntubar majalisar dake shugabancin kasar ba.

Korar da akayi wa ministar harkokin wajen kasar ta Libiya, na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke shirin gudanar da taron kasa da kasa a birnin Paris a ranar 12 ga wata, domin tattauna shirye shiryen zabukan kasar dake tafe na ranar 24 ga watan Disamba.

342/