6 Nuwamba 2021 - 13:24
ECOWAS, Zatayi Taro Gobe Lahadi Kan Batun Mali Da Guinea

Shugabannin kasashe mambobin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika, zasu gudanar da wani taron gaggawa a gobe Lahadi 7 ga watan Nuwamba, domin duba halin da ake ciki a kasashen Mali da kuma Guinea, tun bayan juyin mulkin da sojoji sukayi.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Taron zai maida hankali kan mulkin rikon kwarya a Mali, inda ake ci gaba da fuskantar tada jijiyoyin wuya tsakanin kungiyar ta ECOWAS da kuma sojojin dake rike da mulki, wanda har ya kai ga Malin ta kori wakilin ECOWAS din daga kasar, kan zarginsa da katsan-landan a harkokin cikin gidan kasar.

Kasar Ghana wacce ke rike da shugabancin karba karba na kungiyar ta ECOWAS, ita ce ta kira taron na gaggawa domin duba halin da ake ciki a kasashen biyu inda sojoji ke rikon kwarya.

Kasashen biyu dai na zargin kungiyar ECOWAS, da nuna fifiko idan aka kwantanta da kasar Chadi, inda dan mirigayi Idriss Deby, cewa da Janar Mahamat Deby ya maye gurbin mahaifinsa a kan karagar mulki.

Yayin ziyarar da ya kai a ranar 17 ga wata a Bamako, shugaba Nana Afuko Addo, ya bukaci lalle lalle hukumomin Mali dasu mutunta lokacin da aka tsayar na gudanar da zabe.

A ranar 27 ga watan Fabrairun badi ne aka shirya gudanar da manyan zabukan na Mali, da suka hada da na shugaban kasa, da na ‘yan majalisar dokoki, saidai sojojin dake rike da mulkin na Mali, sun ce suna son gudanar da taron kasa, kafin su tsayar da ranar gudanar da zaben.

342/