1 Nuwamba 2021 - 14:24
Kasashen G20, Sun Amince Manyan Kamfanoni Su Rika Biyan Haraji Na Duniya

Kasashe mafi karfin tattalin arziki na duniya, na gungun G20, sun cimma wata yarjejeniya wacce ta tanadi manyan kamfanoni su rika biyan haraji na duniya da ya kai kashi 15 %, a wani mataki na yaki da kaucewa biyan haraji.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Yarjejeniyar ta tanadi cin tarar manyan kamfanonin daga shekrar 2023, a duk kasashen da suka amince da yarjejeniyar.

Kasashen na G20, sun cimma wannan matsaya ce a taronsu da suka kammala yau Lahadi a birnin Roma na kasar Italiya.

Saidai wasu kasashe irinsu Najeriya da Kenya, da Sri Lanka da kuma Pakistan sun ki amince sanya hannu kan yarjejeniyar.

Shugabannin gwamnatoci da na kasashen G20 sun soma taron kolinsu na kwanaki biyu a birnin Roma na Italiya a ranar Asabar, da zummar duba batutuwan da suka fi daukar hankalin kasashen mafi karfin tattalin arziki na duniya.

Sai dai taron ya gudana ne ba tare da halartar shugabannin Rasha da Chaina ba kai tsaye illa ta hanyar bidiyo.

342/