Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Har ila yau ya kara da cewa gwamnatin Ibrahim Ra’isi tana da mahanga ta musamman kan kasashen gabashi da kuma na Asia. Musamman a loakcin da Iran ta samu damar kasancewa mamba a kungiyar hadinkai ta shanghai.
Babban hafsan sojojin kasa na Kasar Iran Mejo Janaral Mohammad Bagheri ya isa filin saukar jiragen sama na Nukuvo na kasar Rasha ne a jiya lahadi a wata ziyarar aiki da ya kai, inda ya samu tarba daga mataimakin shugaban ma’aikatan gwamatin kasar ta Rasha Sergai Istrakov da sauran manyan jami’an tsoji da mukarraban gwamnatin kasar.
bangarorin biyu sun tattauna tare da musayar ra’ayi kan yadda za su kara fadada danganatar soji dake tsakaninsu , da kuma yadda za’a yi aiki tare wajen tabbabtar da tsaro da kuma yaki da Ta’adanci a yankin.
342/