Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Jaridar Egypt Today ta nakalto Ahmed Attayyib a ganawarsa da shugaban ya na fadar cewa Jami’arsa a shirye take ta hada kai da sauran manya-manyan shuwagabannin addinai a duniya, musamman mazhabar catholica don tabbatar da tsaro da zaman lafiya a bangaren addini a kasashen duniya.
Kafin haka dai shugaban Jami’ar ya gana da paparoma Francis a Vatican inda bangarorin biyu suka cimma matsaya na aiki tare don kawo karshen wuce gona da irin a fagen addini da kuma bunkasa fahintar juna tsakanin mabiya addinai, musamman musulmi da kirista a duniya.
Daga karshe Sheikh Ahmed Attayyib ya bayyana cewa Jami’an Al-azhar ta na da dalibai kimani 30,000 wadanda suka fito daga kasashen duniya fiye da 100.
342/