Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Shafukan yanar gizo na "Al-Sudani" da "Al-Rakuba" sun ce majalisar ministocin ta kafa kwamiti karkashin jagorancin Hamdok da wasu ministoci domin ganawa da bangaren soji, da zimmar ganin an magance rikicin gabashin Sudan, amma sojoji sun ki ganawa da kwamitin a jiya, kuma sun nemi a fara ganawa da Firayim Minista shi kadai kafin kowace irin ganawa da wani minista.
Shafukan yanar gizon sun yi nuni da cewa, bangaren soji ya yi wa Hamdok matsin lamba, domin rusa gwamnati da kafa sabuwar gwamnati, saboda wasu dalilai da sojojin ke gain cewa za su iya tayar da kayar baya.
342/