Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Dama dai Aljeriya ta janye jakadanta a Faransa domin tuntuba, bayan wani furici da aka nakalto shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya yi, game da tarihin samun ‘yancin kan Aljeriya, wanda kuma bai yi wa mahukuntan Aljeriyar dadi ba.
Dama dai an fuskanci tada jijiyoyin wuya tsakanin mahukutan Paris dana Algers bayan da Faransa ta tsauraren matakan bada takardar visa ga ‘yan kasashen Labarawan yankin Magreb ciki har da Aljeriyar.
Faransa dai na amfani da sararin samaniyar Aljeriya, wajen isa ko fita yankin Sahel inda ta ke da dakaru na tawagar Barkhane, saidai ta ce hakan ba zai kawo mata wata matsala ba wajen tafiyar da aikinta ba a yankin.
342/