Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Waziriyar Jamus Angela Merkel, ta ce wannan zabe na da matukar muhimmanci, ta kuma kara da bukatar al'umma da su zabi dan takararta na jam’iyyar CDU a zaben na yau.
Ta roki magoya bayan ta da su bayar da goyan bayan zuwa magajin ta Amin Laschet,wanda ta bayyana cewa zai kare muradun kasar su da kuma ci gaba da ayyukan da ta kaddamar da su a baya.
Za a rufe rumfunan zaben da misalin karfe 6 na yamma.
342/