19 Satumba 2021 - 13:11
​Buhari Ya Tafi Amurka Domin Halartar Babban Taron MDD

A yau Lahadi ne shugaban Najeriya mohammadu Buhari ya kama hanyar zuwa birnin Newyork na Amurka inda zai bi sahun takwarorinsa na duniya wajen halartar babban taron zauren majalisar dinkin duniya karo na 76.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Mai bawa shugaban kasar shawara kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya bayyana cewa a ranar juma’a mai zuwa 24 ga watan Satumbar da muke ciki ne shugaban zai yi jawabi kan babban maudi da za’a yi muhara akai wajen da ya shafi duniya baki daya.

Haka zalika ya kara da cewa shugaban da sauran tawagar dake rufa masa baya za su gana da shuwagabanin da wakilan kasashe da kungiyoyin daban daban a bayan taron, Kuma ana saran zai samu rakiyar ministan harkokin wajen kasar Geoffrey Onyema da kuma Anotni jaral kuma ministan sharia’a na kasa Abubakar malami da kuma karamar minsitan mahalli da dai sauransu.

342/