17 Satumba 2021 - 10:27
Lebanon: Tankunan Daukar Man Disel Daga Iran Sun Fara Shiga Kasar

Tankunan daukar man disel daga kasar Iran, wadanda shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasaralla ya shigo da su ta kasar Siriya sun fara isa kasar Lebanon a yau Alhamis.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Rahotanni sun bayyana cwa Tankunan daukar man disel daga kasar Iran, wanda shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasaralla ya shigo da su kasar ta kasar Siriya sun fara isa kasar ta Lebanon a yau Alhamis.

Tashar talabijin ta Al-Manar ta bayyana cewa mutane sun yi turuwa kan tituna a arewacin kasar don ganin shigowar motocin daukar man. Da wannan kuma kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta kawo karshen takunkumin sayan man Iran da kuma shigo da man zuwa kasar Lebanon

Kafafen watsa labaran kasar ta Labanon sun bayyana cewa aikewa da tankokin dakwan mai da kasar Iran ta yi zuwa kasar Labanon zai bude wani sabon shafin dangantaka tsakanin kasashen Biyu, kuma wani mataki ne na karyar babakeren Amurka a yankin

Tashar talabijin ta Al-Manar ta bayyana cewa mutane sun yi turuwa kan tituna a arewacin kasar don ganin shigowar motocin daukar man. Da wannan kuma kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta kawo karshen takunkumin sayan man Iran da kuma shigo da man zuwa kasar Lebanon.

342/