2 Satumba 2021 - 13:02
​Iran Ta Ce An Rike Kudinta Fiye Da Dala Biliyan 100 A Kasashen Waje Saboda Takunkumin Amurka

Iran ta bayyana cewa yanzu haka tana kudi na cinikin mai da suka haura dala biliyan 100 da ake rike mata a bankuna na kasashen duniya, saboda takunkuman da Amurka ta kakaba mata.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Ministan mai na kasar Iran Jawad Auji ne ya sanar da hakan a jiya a yayin zaman taron kasashen OPEC Plus, inda ya bayyana cewa daga shekara ta 2018 zuwa 2021, an rike kudin Iran a bankuna na kasashen duniya daban-daban da suka haura dala biliyan 100, saboda takunkuman Amurka.

Ya ce baya ga haka kuma adadin gangunan mai da ya kamata Iran ta rika hakowa a kowace a matsayin kasonta na OPEC ya ragu da ganga biliyan 1 da miliyan 800 daga watan Afirilun 2018 zuwa 2021 da muke ciki.

Ministan man na Iran ya jadadda cewa, ya kamata kasashe mambobi na kungiyar OPEC da sauran kasashe na gamayyar OPEC Plus su zama masu ‘yanci a cikin harkokinsu na cinikayya, wanda bai dace kasashe mambobi a OPEC su zama karkashin tasirin takunkuman Amurka, inda a halin yanzu kasashe biyu wadanda das u aka kafa OPEC wato Iran da Venezuela, suna karkashin takunkuman Amurka.

342/