29 Agusta 2021 - 10:23
Ra’isi: Shigo Da Alluran Riga Kafin Covid-19 Ya Rataya Ne Kan Ma’aikatar Kiwon Lafiya

Shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi ya bayyana cewa shigo da alluran riga kafin cutar Covid 19 daga kasashen waje yana karkashin kula na ma’aikatar kiwon lafiyar kasar don tabbatar da ingancin alluran kafin a fara amfani da su kan mutane.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : ya nakalto Ra’isi yana fadar gaka a safiyar yau Asabar a lokacinda yake jagorantar kwamitin yaki da cutar Covid 19 na kasa a nan birnin Tehran.

Ra’isi ya kara da cewa, kasar Iran tana cikin wani mummunan halin dangane da cutar ta Covid 19, don haka ya kara yin kira ga sojoji da kuma wasu kungiyoyin sa kai, da su yi iyakar korarinsu don yaki da wannan cutar, tare da bangaren gwamnati.

342/