Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Har zuw alokacin fasara wadanan labaren babu wani karin bayyani kan dalilin daukar wannan matakin daga hukumomin na Algers , saidia sanin kowa ne dangantaka tsakanin kasashen biyu ta yi tsami a baya bayan nan.
Kafin hakan dai Aljeriya ta sanar a kwanan baya cewa, za ta sake duba alakarta da kasar Morocco, bisa zargin Masarautar da hannu a wutar dajin da ta kashe mutane da dama da lalata dukiya a kasar.
Gomman mutane ne ciki har da sojoji suka rasa rayukansu a wutar dajin wacce ta fara ci tun daga ranar 9 ga wata.
A cewar sanarwar fadar shugaban kasar, ayyukan kiyaya da Morocco ke aikatawa kan Aljeriya, su ne suka tilasta kwakware alakar dake tsakanin kasashen biyu da kuma tsaurara matakan bincike na tsaro a iyakokin yamma.
342/