20 Agusta 2021 - 15:08
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO Ta yi Tir Da Hanzarin Da Kasashe Masu Arziki Suke ke Yi Wajen Samar Da Riga Kafin Cutar Korona

Jami’in kula da agajin gaggawa a hukumar ta WHO Mike Ryan ya nuna takaicinsa game da irin yadda kasashen masu karfin tattalin arziki suke gaggawa wajen samarwa da kasashensu Allurar kamuwa da cutar Korona, adaidai lokacin da miliyoyin mutane a kasashen Duniya ba’a iya yi musu koda Allurar rigakafi ko da sau daya ba,

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA : Yayi wannan bayanin ne jin kadan bayan da gwamnatin Amurka ta sanar da cewa nan ba da jimawa ba za’a sake yi wa Amurkawa Karin rigakafin kamuwa da cutar Korona, ya tabbatar cewa babu wasu dalilai a Kimiyance da ke nuna cewa a kwai bukatar Karin yin Allura adaidai lokacin da wasu da dama suke jira a yi musu ko da sau guda.

Ana sa bangaren shugaban hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhanom ya bayyana cewa rashin nuna Adalci kan rigakafin abin kunya ne ga dukkan dan Adam, kuma idan baa tsaya an magance cutar tare ba, to za’a kara tsawaita yaduwar Annobar a tsawon shekaru, abin da za’a iya shawo kanta cikin watanni idan aka yi aiki tare.

342/